1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rashin adalci a dalilin nuna wariyar launi

Ramatu Garba Baba
April 22, 2021

Britaniya ta nemi afuwa kan rashin karrama sojojin Afirka dana Indiya da suka mutu a yayin taimaka mata a lokacin yakin duniya na daya, bincike ya gano kuskuren da aka yi da gangan.

https://p.dw.com/p/3sQts
Frankreich Thiepval-Denkmal Zeremonie Schlacht an der Somme
Hoto: picture-alliance/PA Wire/G. Fuller

Gwamnatin Britaniya da wani kwamiti na Kungiyar kasashen Commonwealth sun nemi afuwa kan laifin da suka tafka na kin karrama wasu sojojin Afrika da Indiyawa da suka mutu a yayin taimaka wa Britaniya a lokacin yakin duniya na daya, a saboda dalili na wariyar launin fata.

Sun amince tare da neman gafarar, bayan da sakamakon wani bincike da aka fitar a wannan Alhamis, ya gano cewa, ba a yi ma sojin na Afrika da Indiyawa da yawansu ya kai dubu dari da goma sha shida adalci ba, idan aka kwatanta da sauran turawa fararen fata da aka karrama ake kuma ci gaba da girmamawa a duk shekara.  

David Lammy na jam'iyyar Labour a Britaniya, a yayin wani jawabi a zauren majalisar kasar  ''Ya ce babu afuwan da za mu nema da zai kawar da rashin adalcin da aka yi ma wadannan mutanen, amma da wannan afuwa da muka yi, muna mika damar aiki tare don kawar da wannan munmunar babin mu kuma karrama duk wani soja da ya sadaukar da rayuwarsa don kare kasar mu''

Binciken ya nuna cewa, alkaluman wadanda aka manta da su din, ya zarta  za su kai tsakanin dubu arba'in da biyar zuwa dubu hamsin, akasarinsu sun fito daga Indiya da Gabashi da Yammancin Afrika da Masar da kuma Somaliya, duk an ki yi musu adalci a mutunta su tare da karramasu kamar sauran takwarorinsu da suka taimaka ma Britaniyan saboda launin fatarsu.