Rasha za ta ci gaba da kare manufofinta
November 6, 2014Mikhail Gorbachev ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke tattaunawa da kafar yada labarai ta Interfax, inda ya ce zai kare manufofin Putin din da ya bayyana a matsayin gwarzon da ke kare kasarsu a yayin tattaunawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel in ya halarci bukukuwan tunawa da faduwar bangon Berlin da ya yi sandiyyar sake hadewar Jamus a matsayin kasa guda shekaru 25 din da suka gabata da za a gudanar a karshen mako. Mai shekaru 83 a duniya Gorbachev ya taka muhimmiyar rawa wajen faduwar bangon na Berlin da ya yi sanadiyyar sake hadewar Jamus a matsayin kasa dunkulalliya, kuma zai halarci bikin na Berlin ne a dai-dai lokacin da ake zaman doya da manja tsakanin Rasha da kasashen yamma bisa zargin mahukuntan Moscow da su ke yi da hannu a rikicin Ukraine, zargin da Rashan ke musantawa tana mai cewa tana kare muradunta ne kawai a yankin gabashin kasar. Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu dai ta sanya kasashen na yamma kakabawa Rasha takunkumi, inda ake bayyana halin da suke ciki a matsayin mafi wahala tun bayan kammala yakin cacar baka.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman.