Ukraine Rasha ta kara yawan luguden wuta
April 16, 2022Shedun gani da ido sun ce an ga hayaki ya turrnike a ginin ma'aikatar da ke kera tankokin yaki ga sojan Ukraine, kana jami'an tsaro sun hana kowa shiga a ginin.
A wata sanarwar da ta fitar jim kadan bayan harin ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta illata wani kamfanin da ke harhada tankokin yakin Ukraine a wannan Asabar. Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin sa'o'i 24 da dakarun Rasha ke luguden wuta ga wasu kafafen da ke kera makamai a Ukraine, tun bayan wani harin da dakarunta suka kai a wannan Jumma'ar ga kamfanin nan da ke kera makamai masu linzami a matsayin martani, wanda Ukraine ta yi ikrarin kai wa jirgin ruwan Rasha hari da makaman da yake kerawa.
Magajin garin Kiev Vitali Klitschko ya ce duk da yake ya zuwa yanzu baya da adadin illar da farmakin ya yi, ya bukaci mazauna birnin da suka fice da kadda su dawo binrin, inda ya neme su da su kasance a wurin da ke tabbataccen tsaro.