Rasha ta karfafa kawance da Afirka
February 9, 2023Ministan ya ce, kasar Rasha za ta iya karfinta don ganin MDD ta cire takunkumin da aka aza wa kasar Sudan. Sergei Lavrov ya bayyana haka a Khartoum babban birnin kasar Sudan, yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai a Sudan. Ministan harkokin wajen Rasha a ziyarar tasa, ya kuma gana da shugaban kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, inda suka tattauna kan mahimman batutuwa na kara karfafa hulda tsakanin kasashen biyu. Ziyarar kasar Sudan, ita ce kasa ta uku da Lavrov ya ziyarta a Afirka, bayan kasashen Mali da Murtaniya. Kasar Rasha dai na kara karfafa kusancinta da kasashen Afirka, yayin da kasashen Yamma ke gograrin maida ita saniyar ware, ko da a watan jiya ministan harkokin wajen na Rasha Sargei Lavrov ya ziyarce kasashen Eritrea, Angola, Eswatini Afirka ta Kudu. A Watan Juli kuwa za a yi taron hadakar Rasha da kasashen Nahiyar Afirka.