1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ranar dimukuradiyya karo na 25

June 12, 2024

Bayan shafe tsawon shekaru 25 ana ta gwadawa, Tarayyar Najeriya na bikin ranar dimukuradiyya a kasar amma cikin matsi da ma rashin tsaro mai zafi.

https://p.dw.com/p/4gyC5
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Ranar Dimukuradiyya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

An dai yi fareti an kuma yanka alkaki na biki, a bangaren shugabannin Tarayyar Najeriya da ke biki da Owambe da nufin cika 25 a cikin tsarin siyasar Yamma. Bikin kuma da ke zaman babbar dama ta tunawa da gwarazan da suka tunkari sojoji cikin kasar, kan hanyar sake girka tsarin na dimukuradiyyar da ke zaman abun alfaharin 'yan bokon kasar. Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya dauki lokaci yana jawabi ga kasa, jawabin kuma da ya mai da hankali wajen kiran sunayen gwarazan kungiyar NADECO da tai fafutukar tabbatar da zaben shugaban kasa a 1993. Shugaba Tinubun dai ya ce zai yi gwargwadon karfinsa, ya kare tsarin da ya bayar da 'yanci daga kama-karyar baya.

Najeriya | Naira | Daraja
Darajar kudin Najeriya Naira, na hawa da saukaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kai wa ga kare dimukuradiyya a cikin halin yunwa ko kuma tunkarar biyan bukata ta ciki dai, shugaban ya kuma ta'allaka rikicin tattalin arzikin kasar da kawar da kai, a kan kokarin kwaskwarima a tsarin tattalin arzikin kasar da ke lalace. Duk da cewar dai bai fito fili ya bayyana dalla-dalla ba, shugaban kuma a karon farko a ayyana cimma yarjejeniya da 'yan kodagon kasar a kan batun mafi karancin albashi. Koma ya zuwa ina Tinubu ke shirin ya kai a kokarin burge al'ummurar Najeriyar, jawabin nasa na nufin abubuwa dabam-dabam ga 'yan kasar a halin yanzu. A yayin da masu mulkin kasar suke fadin ta yi fari tana shirin yin zaki, masu fafutuka dai na can na jerin zanga-zangar adawa a kan manufofin gwamnatin kasar da suke fadin sun dau kasar zuwa bakin duhu a halin yanzu.