1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar addu'oi na musamman ga Mandela

Englisch-redDecember 10, 2013

Kawo yanzu shugabannin kasashen duniya sun fara hallara a kasar Afirka ta Kudu, domin halartar jana'izar marigayi tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

https://p.dw.com/p/1AVtK
Hoto: Reuters

Za dai a a gudanar da addu'oi na musamman domin tunawa da girmamawa ga Mandela da Allah yayi wa cikawa a ranar Alhamis din makon jiya a filin wasa na birnin Johannesburg, yayin da ake sa ran shugaban Amirka Barack Obama da tuni ya isa Afirka ta Kudun da kuma na kasar Cuba Raul Castro za su gabatar da jawabai a lokacin addu'oin.

Shima shugaban kasar Jamus Joachim Gauck na daga cikin shugabannin kasashen duniya da za su halarci addu'oin musamman din da aka shirya.

A Talatar nan ne dai ake gudanr da addu'oin na musamman, kuma tayi dai dai da ranar bukuwan kare 'yancin dan Adam da Majalisar Dinkin Duniya ta ware. Wanda a dangane da haka ne Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, zai gabatar da jawabinsa inda zai bada misalai a kan dabi'un marigayi Mandela na gaskiya da rikon amana da kuma kare hakkin dan Adam, domin ayi koyi dasu a samu ci gaban duniya baki daya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu