1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan Amnesty kan yankin Niger Delta a Nigeria

Zainab A MohammadNovember 3, 2005
https://p.dw.com/p/Bu4T

MOD.:Shekaru 10 bayan kasha sanannen marubucin nan kuma mai fafutukar kare hakkin biladama a tarayyar Nigeria Ken Saro Wiwa da wasu mutane 8,akwai shaidu masu yawan gasket dake nuni dacewa har yanzualummomin yankin Niger-Delta mai arzikin mai a Nigeria na fuskatar barazanar rasa rayukansu dai dai ta hannun jamian tsaro.Wannan bayanin na kunshe ne cikin rahotan kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International.

Rahotan kungiyar kare hakkin jamaa na Amnesty International ya fito ne mako guda kafin cikan shekaru 10 da kashe Ken Saro Wiwa da mukarrabansa,wadanda aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarata 1995,akarshin zartarwar gwamnatin mulkin sojin Nigeria na wancan lokaci.

Saro Wiwa dai ya kaddamar da kamfaign na adawa da kanfanin man nan na Anglo-Dutch da akafi sani da suna Shell,masanaantar da injishi ta haifar da mummunan yanayi a lardin ogoni marasa rinjaye,ba tare da bayarda wani gudummowa na raya karkara ba.

To sai dai Directan kungiyasr Amnesty sashin Afrika Kolawole Olaniyan yace shekaru 10 bayan zartar da wannan hukuncin kisa ,har yanzu babu wani abun kuzo kugani na gajiya da alummar niger delta suka samu,ayayinda a kullum jamian tsaro ke dauki daya daya da rayukansu.

Rahotan kungiyar kare hakkin Jamaan dai ya mayar da hankali ne kan wasu hadurruka biyu da suka wakana,inda akayi amfani da jamian tsaro wajen afkawa alummomin kauyuka,saboda sun kalubalanci manyan kamfanonin mai biyu na shell da kuma Shevron na Amurka dake gudanar da aiki a yankin.

A ranar 4 ga watan Febrairun wannan shekara nedai yan sanda suka bindige har lahira mutum guda tare da raunana wasdu 30,ayayinda alummomin kauyen Ugborodo suka kai mamaye a cibiyar Chevron dake yankinsu.

Makonni biyu kachal bayan wannan,ranar 19 ga watan na Febrairu akalla wasu mutane 17 sun gamu da ajalinsu ,lokacin da dakarun tsaro na hadin gwiwa dake kare naurorin kamfanin man suka kai somame a garin Odioma,inda suka kone fiye da rabin kauyen,a sunan suna neman yan tawaye.

A dangasne da hakane yanzu haka kungiyasr Amnesty Int take kira ga gwamnatin Nigeria data gudanar da bincike tsaurara a dangane da wadannan kisan gilla da jamian tsaronta ke cigaba da aiwatarwa akan fararen hula,tare da lalata kayayyakinsu ba tare da wani dalili ba.

Bugu da kari Amnesty ta kuma bukaci hukumar gudanarda Kamfanin Chevron,data kafa hukumar bincike mai zaman kanta,wadda zata binciki irin rawa da kamfanin man ya taka cikin wadannan yamutsi guda biyu.