Rabon gadon marigayi Nelson Mandela
February 3, 2014Masu tafiyar da kadarorin marigayi tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela sun sanar da cewa ya bar kimanin dalar Amirka miliyan 4 da dubu dari kwatankwacin kimanin naira miliyan dari 6 a kudin Najeriya, kuma wadanda za su gaje shi cikin wasiyarsa sun hadar da iyalansa da ma'aikatansa da makarantun da ya halarta da jam'iyyarsa ta ANC da ta kunshi wadanda suka yi gwagwarmayar kawo karshen mulkin wariyar launin fata na Turawa tsiraru, wadda kuma take mulki a kasar ta Afirka ta Kudu a yanzu haka.
Daraktan kula da kadarorin marigayi Mandelan Dikgang Moseneke ne ya sanar da hakan, inda ya ce an karanta wasiyar Mandelan ga iyalansa, sai dai ya ce adadin kudin ka iya canzawa a yayin da ake ci gaba da yin nazari na tsanaki kan wasiyar da Mandelan ya rubuta gabanin rasuwarsa.
Mandela dake zaman shugaban kasar Afirka ta Kudu bakar fata na farko da yayi gwagwarmayar kwatar 'yan cin bakaken fatar kasar, ya rigamu gidan gaskiya ne a ranar 5 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2013 yana da shekaru 95 a duniya bayan ya sha fama da jinyar da take da nasaba da huhu.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal