1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Platzeck ya yi murabus a matsayin shugaban SPD

Mohammad Nasiru AwalApril 11, 2006

Dalilai na rashin lafiya suka shi ajiye wannan mukami.

https://p.dw.com/p/Bu0g
Matthias Platzeck
Matthias PlatzeckHoto: AP

Duk da cewa jam´iyar ta SPD na cikin gwamnatin kawance karkashin jagorancin Angela Merkel bayan kayen da ta sha a zaben ´yan majalisar dokoki ta Bundestag farin jininta ke raguwa a idanun jama´a. Hasali ma yanzu tana shan matsin lamba ne kan yadda zata sake tsara manufofinta a cikin babban gwamnatin kawance don samun goyon bayan masu zabe. Hakan kuwa na faruwa ne a cikin wani yanayi na karancin shugabanni wanda ya kara yin muni sakamakon murabus din da Matthias Platzeck ya yi a matsayin shugaban jam´iyar ta SPD.

Idan aka tabbatar da nadin Firimiyan jihar Rheinland Palatinate Kurt Beck a matsayin magajin Platzeck a gun babban taron da jam´iyar zata yi a karshen watan mayu, shi ne zai zama shugaban SPD na biyar a cikin shekaru 7. A karshen shekarar 1999 Oskar Lafontaine wanda ya kasance mutumin da ya ceto jam´iyar ya sauka daga mukamin shugabanta. Bayan sa tsohon shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya karbi ragamar shugabancin jam´iyar inda ya dora ta akan alkiblar tattalin arziki da gwamnatinsa ke bi. Bayan jerin kayen da jam´iyar ta sha a zabukan kananan hukumomi a farkon shekara ta 2004 dole Schröder ya mikawa Franz Müntefering wannan mukami. Amma bayan zaben ´yan majalisar dokoki, jam´iyar ta fara juyawa Müntefering baya, wanda shi ma a karshe ya jefa tawul, musamman bayan da ´ya´yan jam´iyar suka ki amincewa da mutumin da Müntefering din ya so gaje shi wato Kajo Wasserhövel.

Mutane da dama sun so da Firimiyan jihar Rheinland Palatinate wato Kurt Beck ya gaji Müntefering amma ya ki wannan tayi, saboda zaben ´yan majalisar dokokin jihar sa da ya sa ma ido a cikin watan maris. Saboda babu zabi ya sa jam´iyar ta dorawa Mathias Platzeck wannan nauyi, wanda a halin yanzu ya ce gaskiya kam ya yi masa yawa, saboda bai da karfin daukar wannan nauyi.

Watanni kalilan bayan an nada shi Platzeck ya taka rawar gani, inda ya tashi daga matsayi wani dan siyasa da ba´a san shi ba sosai zuwa dan siyasa na biyu mafi farin jini baya ga SG Angela Merkel. Platzeck ya kasance mutum mai hakuri da natsuwa wanda ke kwantar da hankalin shugabannin jam´iyar ta SPD. Shi ma Kurt Beck ana yi masa shaida ta sanin makaman aiki da iya shugabanci. Ko shakka babu yanzu SPD za ta goyawa Beck baya domin ba ta da wani wanda za ta danka masa wannan aiki na jagoran jam´iya.