Atiku zai kalubalanci sakamakon zabe a kotu
February 27, 2019Mai shekaru saba'in da biyu da haihuwa, Atiku ya ce akwai yankunan kasar da aka tabbatar da an tafka magudi. Ya kara da cewa a tsawon shekarun da ya kasance a fagen siyasa, bai taba ganin irin koma baya a demokradiyar Najeriya kamar yadda ya gani a zaben na ranar Asabar ba.
A daya bangaren kuwa, wasu 'yan kasar na ci gaba da baiyana farin cikinsu kan nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu. Shugaba Buhari, a yayin jawabinsa na farko bayan lashe zaben, ya godewa dinbin al'ummar kasar da suka zabe shi da kuma amanar da suka ba shi kan ya ci gaba da jagorantarsu. Buhari dai ya lashe zaben da kashi hamsin da shida cikin dari na kuri'un da aka kada, yayin da Atiku ya zo na biyu da kashi arba'in da daya cikin dari na kuri'un.
Duk da cewa masu sa ido kan zaben daga kasashen waje, sun ce an gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba, hadakar kungiyar kare hakkin bil adama a Najeriya, ta ce mutum akalla talatin da tara ne suka mutu a ranar zabe a sassan Najeriyar.