1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adamawa: PDP ta doke APC a zaben gwamna

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2019

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Adamawa bayan kammala sake zaben cike gurbi a wasu kananan hukumomi 14 na jihar.

https://p.dw.com/p/3FrVD
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Adamawa ta ayyana Fintiri a matsayin zababben gwamna da yawan kuri'u dubu 376,552 kamar yadda babban baturen zaben jihar Prof. Andrew Haruna ya tabbatar.

Fintiri da ke zama tsohon kakakin majalisar jihar Adamawa kuma tsohon mukaddashin gwamnan jihar, ya doke sauran 'yan takara 29 da suka fafata neman kujerar gwamna ciki har da gwamna mai ci Bindow Umar Jibrilla na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 336,386 a zaben kuma shi ne na biyu, jam'iyyar ADC wanda Abdul'aziz Murtala Nyako ya yi wa takara ta zo ta uku da kuri'u 113,237.

A baya babbar kotun jihar Adamawa ta bayar da umurnin dakatar da gudanar da karashen zaben gwamnan a jihar bayan da dan takarar Jam'iyyar MRDD ya kalubalanci hukumar INEC na rashin sanya alamar jam'iyyarsa a takardar zaben da ya gudana a farko kamin daga bisani wata kotu a jihar ta sauya matsayarta bisa umarnin da ta bayar na dakatar da kammala zaben.

Sai dai dama jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta kalubalanci hukumar INEC kan rashin tuntubarta kamin sanya ranar sake zaben cike gurbin. Kawo lokacin rubuta wannan labari babu wani martani na amincewa da sakamakon zaben ko yin watsi da shi daga bangaren gwamnatin jihar.