1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta bukaci MDD ta ja kunnen India

Abdullahi Tanko Bala
August 6, 2019

Matakin India na janye kwarya kwaryar cin gashin kai na yankin Kashmir ya haifar da zaman zulumi a yankin.

https://p.dw.com/p/3NT6h
Indien Kaschmir-Konflikt nach Änderung Artikel 370
Hoto: AFP/R. Bakshi

Firaministan Pakistan Imran Khan ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya su dakatar da India daga karbe ikon kwarya kwaryar cin gashin kai ga yankin Kashmir, yana mai cewa zai bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kotun kasa da kasa su dakatar da wannan mataki. 

'Yan majalisar dokokin India a yau talata sun kada kuri'ar janye kwarya kwayar cin gashin kai na yankin Kashmir da ke da rinjayen muslmi wanda ke karshin gudanarwar kasar India.

Jam'iyyar Firaministan Narendra Modi da ke mulkin India ta gabatar da kudirin sake fasalin yankunan Jammu da Kashmir wanda majalisar ta kada kuri'a akai kwana guda bayan kudirin shugaban kasa da ya soke sashe na 370 na kundin tsarin mulkin da ya baiwa yankin Kashmir kwarya kwaryar cin gashin kai.

Matakin dai ya haifar da fargaba tsaro a yankin.Takaddama kan rikicin yankin Kashmir ya kai kasashen biyu na India da Pakistan da ke makwabtaka da juna gwabza yaki har sau biyu tun bayan da suka sami yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.