Pakistan na fuskantar karancin abinci
September 12, 2022Talla
A yayin wata tattaunawa da shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya da yake masa godiya bisa tallafin abinci da kayayaki sawa gami da rumfuna, Firaminista Sharif ya nuna bukatar samun taimakon gagawa daga kasashen duniya.
Mutum sama da dubu 600 ne da suka hada da mata da kananan yara ke cikin yanayi na bukatar taimako sakamakon bala'in ambaliyar ruwa da 'yan kasar suka ce ba su taba ganin irinta ba.
Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji masu zaman kansu na ci gaba da fadi tashin isar da kayayakin taimako ga al'ummar kasar.