Takaddama tsakanin Pakistan a Indiya a kan Kashmir
August 15, 2019Talla
A yayin da kasashen Indiya da Pakistan ke yin bukukuwan shekaru 72 na samun 'yancin kai, a yankin Kashmir kuwa, sabuwar kuntata wa jama'a ce aka bullo da ita. Tun yakin da aka gwabza tsakanin kasashen Indiya da Pakistan a shekara ta 1947 izuwa 1949, aka raba yankin na Kashmir gida biyu, inda daya bangaren ke karkashin Indiya yayin daya bangaren ke karkashin Pakistan. Tuni ma da yaki ya barke tsakanin kasashen biyu, inda kafin hada wannan rahoton, labarai suka tabbatar da mutuwar sojojin Pakistan uku yayin da sojojin Indiya biyar suka mutu a gumurzun da kasashen biyu suka yi.