Harin bam ya kashe mutane a Islamiyya
October 27, 2020Talla
Wani jami'in dan sanda a yankin Peshawar da lamarin ya faru Waqar Azim yace mutane fiye da 60 ne suke daukar darussa a lokacin da bam din ya fashe.
Yace wanda ya ajiye bam din a cikin wani kunshin kaya ya fice kafin bam din ya tashi. Dalibai 34 ciki har da malamai biyu suka sami raunuka a harin. Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Gundumar Peshawar da lamarin ya faru ya yi kaurin suna wajen yawaitar hare hare a pakistan inda masu ikrarin jihadi ke kai hari akan jami'an tsaro.