1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ouattara ya ce ba zai nemi tazarce ba

Abdullahi Tanko Bala
March 5, 2020

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba bayan tsawon lokaci ana ta rade-radi game da makomarsa a siyasance

https://p.dw.com/p/3Yugm
Elfenbeinküste Präsidentschaftswahl Alassane Ouattara
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Shugaba Alassane Ouattara a wannan Alhamis din ya kawo karshen rade-radin da ake yi a game da ko zai sake tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a zabe mai zuwa a watan Oktoba..

" Yace na sanar a ranar da aka yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska cewa ba zan nemi wani wa'adin mulki ba. Saboda haka zan yi amfani da damar da na samu a yau cewa na yanke shawarar ba zan tsaya takarar shugabancin kasa a zaben 31 ga Oktoba 2020 ba, zan mika mulki ga masu karancin shekaru.”

A can baya dai Ouattara yace zai tsaya takara idan manyan abokin hamaiyarsa suka nemi tsayawa takara.