Omar Bango ya kwanta dama.
June 8, 2009Kamar yadda mayan addinai suka bayyana,duk mai rai zai ɗanɗana mutuwa.A jiya ne shugaba ƙasar Gabon Haj Omar Bango Ondimba ya
kwanta dama bayan shekaru fiye da 40 ya na jagorancin ƙasar.
An haifi Albert Bernard Bongo, ɗan ƙabilar Bateke,ranar 30 ga watan Disemba na shekara ta 1935.
Bayan ya kamalla karatun a birnin Brazaville na ƙasar Kongo ya fara taka rawar siyasa a opishin ministan harakokin wajen ƙasar Gabon tun samun´yancin kan ƙasa.
Daga bisani ya shiga fadar shugaban ƙasar Gabon na farko Leon Mba, inda ya taka mahimmiyar rawa.
Hakan ya sa a ka aiyyanar da shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a shekara ta 1966.
Bongo ya hau kujera shugabacin Gabon ranar 28 ga watan Nowmba bayan mutuwar shugaba Leon Mba.
Da shekara ta zagayo ya girka jam´iyar PDG wato Parti Democratique Gabonais.
Bayan kaɗawar iskan demokraɗiya a Afrika,a farkon shekarun 1990, shugaban ƙasar Gabon ya bada damar girka jam´iyun siyasa.
Saidai a duk lokacin da aka shirya zaɓe jam´iyarsa ta PDG ke wa sauran fintikau.
A shekara ta 1973, ya shiga addinin musulunci, ya kuma ɗauki sunan Haj Omar Bango Ombinba.
Firaministan ƙasar ne Jean Eyeghe Ndong, ya bayyana sanarwar rasuwar shugaban ƙasa a wata asibiti dake birnin Bacelona na ƙasar Spain bayan yayi fama da cutar kansa.
Sanarwar ta gayaci al´umomin ƙasar Gabon kimanin miliyan ɗaya da rabi su shiga zamnakoki na wata guda.
Injiniya Maman Mati, wani mazaunin ƙasar Gabon, yayi kyakkyawan yabo ga shugaban Omar Bago a game da rawar da ya taka ta fannin inganta rayuwar talakawa.
Tun dai kamin mutuwar shugaba Haj Omar Bango Ondimba, ƙasar Gabon na fama da rikicin siyasa inda ´yan adawa ke zarginsa da mulkin kama karya.A yanzu babbar aya tamba da ´yan Gabon ke ci gaba da yi itace, wanene zai gaji shugaban mafi yawan shekaru a gadon mulki a nahiyar Afrika ?
Idan dai akayi yi amfani da dokokin ƙasa, shugabar Majalisar dattaɓai ya kamata ta hau mulkin wucin gadi , sannan ta shirya zaɓe a tsukin watani ukku, to saidai akwai raɗe raɗi masu yawa, dake nunar da cewar Ministan tsaro, ɗan mirganyin shugaban ƙasa wato Ali ben Bongo, zai karɓi ragamar mulki.Ko dai ƙaƙa zata kasance, kwanaki na gaba zasu bayyana haske.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.
Edita: Mohamed Nasiru Awal