1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olusegun Obasanjo ya ce zai yi nisa da PDP

January 13, 2014

Ɗaukan matakin da tsohon shugaban ƙasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi na dakatar da duk wasu harkokinsa a jam'iyyar PDP mai mulkin ƙasar ya bar baya da ƙura.

https://p.dw.com/p/1Apwg
Porträt - Olusegun Obasanjo
Hoto: Getty Images

Guguwar rikici da taƙaddama a tsakanin tsohon shugaban Najeriyar Cif Olusegun Obasanjo da ke zama jigo kuma mai ikon faɗa a ji a jam'iyyar ta PDP lamari ne da ya ɗauki dogon lokaci yana bayyana kansa, domin kuwa taƙaddamar da kai tsaye ake danganatata da raba garin da suka yi da Shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan da ke zama yaron gidan Obasanjo. Ta fito fili ne a lokacin da Obasanjo ya sanar da ajiye muƙamminsa na shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP a yanayi na bazata.

Takun saƙa tsakanin 'yan jam'iyyar ta PDP a kan wannan mataki

Sannu a hankali rikici ya ci gaba da ƙara rincaɓewa maimakon gyara musamman yadda jam'iyyar PDP ta rinƙa yi wa dukkanin masu goyon bayan Obasanjo fyaɗen ya'yyan kaɗanya daga muƙaman da suke riƙe da su a jam'iyyar PDP. Matakin baya baya nan shi ne na sanar da a jingine dukkanin al'amMura da suka shafi PDP. Ko wannan zai yi wa jam'iyyar wani tasiri a halin rikicin da ta ke ciki ? Malam Hassan Sardauna mai sharhi ne a hakokin yau da kullum.Ya ce :''To a harakar PDP a yau ba gobe ba, ko wanene ba zai ce Obasanjo ba kowa ba ne, saboda haka wannan mataki zai yi wa jam'iyyar PDP illa domin ku wa duk wanda ke jam'iyyar PDP a yanzu in dai bai ce shi ɗan Obasanjo ba ne, to ya kuwa yi wa da shi wanda ya zama uba.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Rikicin ya yi ƙamari a cikin jam'iyyar ta PDP mai mulki

A bayyana yake a fili cewa Cif Obasanjo ya fusata da yadda ake tafiyar da al'ammura a jam'iyyarsu ta PDP abin da ya sanya shi kai wa ga fito wa fili ya rubuta doguwar wasiƙa zuwa ga shugaba Jonathan wacce ya yi wa taken tun kafin a makara. To sai dai haba'haban da aka ga yana yi da wasu gwamonin jam'iyyar PDP da suke yi wa shugaba Jonatahan tawaye, inda har wasu suka koma jam'iyyar adawa ta APC ya sanya jefa alamar tambaya a kan inda ya dosa da ma makomar wannan mataki. To sai dai wannan matakai ne da ake wa kalon na janye jiki da tsohon shugaban Najeriyar ke yi daga jam'iyyar da ma gwamnati da shi ne ya yi tsaye wajen tabbatuwarta a 2011. Abin da ya sanya Alhaji Umar Bello Calculate jigo a jam'iyyar PDP bayyana cewar akwai abin da fa wannan ke nufi.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria Fernsehansprache ARCHIV
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

‘'Ni a nawa fahimta babu shakka zawarcin da aka yi masa ya yarda da ita ke nan, don haka dolle ne ya share fagen faruwan haka. Obasanjo duk inda ka same shi babu shakka zai iya kawo maka illa a fagenka na rayuwa. Dukkanin ƙoƙarin da na yi domin jin ta bakin kakakin tsohon Cif Obasanjon ya ci tura, domin kuwa shi kansa tsohon baya ma a cikin Najeriyar a halin yanzu. A yayin da Cif Obasanjon bai ɓoye inda ya dosa ba a kan matsayinsa a jam'iyyar ta PDP da alamun da sauran kallo a gaba, musamman yadda shi bai ce ya fice daga jam'iyyar ba. Amma kuma ya dakatar da shiga duka harkokinta a yanayin da zai sa ya zame mata ƙandagaren bakin tulu, musamman a rigingimun da take fuskanta da suka fi kowane muni tun kafuwarta a Najeriyar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da Ubale Musa ya aiko mana a kan taron jam'iyyar ta PDP

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane