1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz ne dan takaran SPD

November 25, 2024

Jam'iyar SPD da ke a kasar Jamus ta zabi Olaf Scholz da ya kasance dan takaranta a zaben kasar da ke tafe yanzu haka Scholz na jagorantar gwamnatin kawancen jam'iyyu uku kuma kawancen da ya rushe a farkon watannan

https://p.dw.com/p/4nPFo
Deutschland Berlin 2024 | SPD nominiert Kanzler Scholz als Kandidaten | Rede Olaf Scholz
Hoto: Annegret Hilse/REUTERS

Don haka yanzu Olaf Scholz shi ne zai fiskanci babbar jam'iyyar adawa ta CDU wacce kusan shekaru 16 take mulki Jamus karkashin Angela Merkel kafin zaben kasar da ya gabata. A bisa tsari dai zaben Jamus na da sauran lokaci, domin kamata ya yi har sai karshen watan Satumban badi ne,  amma rikicin cikin gida na jam'iyyu da kuma yadda a zabukan wasu jihohi aka ga dukkan manyan jam'iyyun kasar na mummunar faduwa ya yinda masu tsattsauran ra'ayi ke samu nasara, hakan ne ya tilasta kiran yin zabe da wuri. Inda yanzu aka shirya gudanar da zaben a watan Febrairun badi, wato nan da watanni uku. Hauhawar farashi da tsadar rayuwa da wadanda ake gani suna alaka da yakin Ukraine da Rasha suna daga cikin abinda ya dagula siyasar kasar ta Jamus. Dama dai yan jam'iyar SPD sun so tsayar da ministan tsaron kasar Boris Pistorius, wanda shi kuma yace a kai kasuwa, abin da ya sa Olaf Scholz ya zama dantakarar da ba wata babbar hamayya. Yanzu dai taron jam'iyar da zai gudana a farkon watan Junairu shi ne a hukumance zai tabbatar da zaben na Olaf Scholz a matsayin dan takaransu.