1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya yi kira ga Musulmin kasar Amirka

Salissoi BoukariFebruary 19, 2015

A wani zaman taro kan harkokin tsaro da ke gudana a birnin Washington na Amirka, Shugaba Obama ya yi kira ga Musulmin kasar da su yaki masu tsatsauran ra'ayin adini.

https://p.dw.com/p/1EeMt
Hoto: AP

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya yi kira ga Musulmin kasar da su yaki duk wani salo na masu tsattsauran ra'ayin adini, inda ya ce ba wai su na yaki ba ne da adinin Muslunci, amma kuma suna yaki ne da masu canza akidar Muslunci ta hanyar sanya masa wasu akidojin wanda adinin da kansa bai yarda da su ba. Obama ya yi wadannan kalamai ne a kwana na biyu na babban zaman taron kwanaki uku da kasar ta Amirka ta kira kan harkokin tsaro a birnin Washington.

Obama ya kara da cewa jagorori irin na kungiyar IS ba jagorori ba ne na Muslunci kawai 'yan ta'adda ne, inda ya ce kuma ba wai suna magana ba ne da sunan Musulmin duniya baki daya ba. Shugaba Obama ya kara da cewa hare-haren da suke kaiwa kan 'yan kungiyar ta IS ba wai ita ce kadai hanya ta yakar ta'addanci ko masu tsauraran ra'ayi ba. Kungiyar ta IS dai na amfani ne da hanyar sadarwa inda take aika sakwanni kai tsaye zuwa ga matasa da zummar birkita musu kwakwalwa.