1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Norway ta rufe ofishin jakadancinta a yankin Palasdiwa

February 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9k

Kasar Norway ta rufe ofishinta na jakadanci ga jamaa dake yankin palasdiwa a gabar yamma bayanda wasu kungiyoyin gwagwarmaya na palasdiwa sukayi barazar kaddamarwa yan kasashen ta da na Denmark da kuma yan kasashen faransa akan zanen rahannanan na muzanta annnabi Muhammad(s.a w) da wata jaridar Denmark ta buga.

Yan bindigar palasdiwa na kungiyoyin Islamic Jihad da na kungiyar Fatah sun kewaye ofisoshin kungiyar gamayyar turai suna harbi cikin iska inda suke bukatar kungiyar data nemi gafarar musulmi akan lamarin.

A kasar Indonesia ma wasu daruruwan musulmi sunyi cuncurundo suka datse kofar ofishin gwamnan lardin Sulawesi a dai dai a lokacinda babban sakataren kungiyar Red Cross na kasar Denmark jorgen paulsen ya kai wata ziyara.

Mr Paulsen din dai a lokacinda yake jawabi ga masu zanga zangar dai ya bayyana wannan abu da jaridar ta kasar sa tayi da cewa sakarci ne sai dai kuma yakara dacewa yancin yan jarida abune da gwamnatin kasar tasu ba zata iya hanawa ba.