Norway ta kosa da halayar ´yan tawayen Sri Lanka
June 9, 2006Talla
Bayan sabon koma-bayan da aka samu a kokarin samar da zaman lafiya a Sri Lanka, kasar Norway ta saka ayar tambaya game da ci-gaba da shiga tsakanin don yin sulhu tsakanin gwamnatin Sri Lanka da ´yan tawaye. Wata sanarwa da ta fito birnin Oslo ta ce za´a bukaci gwamnatin Sri Lanka da kuma ´yan tawayen Tamil Tigers da su nuna matsayin su a rubuce. Sanarwar ta gwamnati a birnin Oslo ta ce a cikin wannan takarda dole ne bangarorin biyu su nuna ko suna son a ci-gaba da shirye shiryen samar da zaman lafiyar. Bayan nan ne Norway zata yanke tata shawarar. A jiya alhamis wakilan ´yan tawayen Tamil Tigers sun ki halartar taron samar da zaman lafiyar saboda a cewarsu ba sa son su zauna kan teburi guda da membobin gwamnatin Sri Lanka.