Nok - Gano abun al'ajabi a yammacin Afirka
Wasu gumaka masu dinbin tarihi da mazauna yankin Nok na jihar Kaduna a Najeriya suka gina. Masana kan ilimin karkashin kasa ba su gano dalilin gina su ba. An baje kolinsu a gidan tarihi na birnin Frankfurt a nan Jamus.
Nok - Tushen gumakan al'adar Afirka
An baje kolin wadannan kayayyaki da ke da dinbin tarihi na sama da shekaru 2000 na Nok a gidan tarihi na birnin Frankfurt da ke nan Jamus tun daga 30 ga watan Oktoban shekarar 2013 zuwa 23 ga watan Maris na 2014. Wannan shi ne karo na farko da gidan tarihin na birnin Frankfurt ya baje kolin daya daga cikin dadaddun al'adun kasashen yankin Kudu da Saharar Afirka.
Fargaba kan ci gaba da sace gumakan
An fara gano gumakan na al'adar yankin “Nok“ a garin Jos babban birnin jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya. A shekarar 1928 ne aka fara gano gunki na farko. Tun daga shekarar 2005 ne tawagar masana kan ilimin karkashin kasa daga Jamus da Najeriya suka fara gano wadannan kayayyakin tarihin inda suka gano su a gurare sama da 200. Sai dai har yanzu ana fuskantar matsalar sace su.
Dadaddun kayayyakin tarihi gabanin kafa Najeriya
Bayan wani aiki tukuru mai wahala da aka gudanar na hako gumakan, masana ilimin karkashin kasa sun yi kokarin harhadasu domin mayar da su yadda suke tun asali. Wasu daga cikin kayan da aka gano sun hadar da kalangu da duwatsu da kuma kayan ado wanda ya kayatar da masanan sosai. Tarihi ya nunar da cewa wadannan kayan tarihin na al'adar Nok an yi su ne gabanin kafa Najeriya gurin da suke a yanzu.
Shin ko tsofaffin kayan kira ne na dan Adam?
Wani murhu da aka tono na nuni da dadaddun kayan kira a tarihin rayuwar dan Adam. An gano gumakan da kuma wasu kayan aikin da suka gina na nuni da wani aiki na kere-kere da suka afku sama da shekaru 500 a wannan yankin. Masanan sun gano cewa wadannan kayan al'adar na yankin Nok da aka kera an yi su ne shekaru 500 kafin zuwan Annabi Issa (A.S).
Babu tabbas a kan yadda aka yi amfani da su
Har yanzu jita-jita ce kawai ake yi dangane da amfanin da aka yi da su. Masu bincike na ganin an yi amfani da su ne wajen yin tsafi. Sun ce binne sun da aka yi wani bangare ne na tsafin. A wasu ramukan an tono daruruwan kananan abubuwa sai dai saboda kankantar su an kasa gano ko mene ne. Masu binciken na ganin da gangan aka lalatasu domin kada a gane ko mene ne a sake hadasu.
Siffar mutane da dabbobi da kuma siffar mutum da dabba a hade
Wani abun al'ajabi shi ne yadda aka kera wasu gumakan. An yi wa wasu manyan idanu wasu kuma kanana. Idanunsu ba a zagaye suke ba irin na mutane, wasu na da katon baki wasu kuma na da dogayen hakora. Askin wasunsu na daban ne ga wasu da dogon gemu wasu kuma an yi musu ado da kayan kawa. Wasunsu sun rufe kawunansu. Yayin da wasu ke da siffar mutane wasu kuwa na da siffar mutum da dabba a hade.
Abin sha'awa ga Picasso da sauran masu fasahar zane-zane
Lokacin da wadannan gumaka na al'adar yankin Nok suka iso nahiyar Turai a farkon karni na 20 sun dauki hankali sosai ga masu fasahar zane da kuma da yawa daga cikin Turawa. Yayin da wasu ke ganin abun banbarakwai, ga masu fasahar zane-zane irin su Paul Gaugin da Pablo Picasso ko kuma Ernst Ludwig Kirchner na ganin su a matsayin abun sha'awa domin sun gano wani sirri daga gumakan na Afirka.
Abu mai muhimmanci ga tarihi a duniya
Kasashen duniya da dama na bukatar wadannan gumaka masu tarihi. Tun tsawon lokaci an yi kokari matuka wajen ganin an baje kolinsu a gidajen kayayyakin tarihi a duniya. A yanzu haka akwai irin wadannan kayan tarihi a gidajen tarihi da dama. Misali a Paris da London da kuma birnin New York. Za a samu wadannan kayan al'ada a manyan gidajen tarihi na duniya baki daya.
Wasu na tono su da kuma sayar da su ta barauniyar hanya
Kasancewar ana bukatar wadannan kayan tarihi na al'adar yankin Nok a kasuwannin kayan tarihi na duniya baki daya ya sanya ake samun dillalai da ke hako su ta barauniyar hanya domin sayar da su a kan miliyoyin kudi na Euro a kasashen Turai. Da dama daga cikinsu sun iso gidajen tarihi na Turai ta irin wannan hanya. Amma wadanda ke gidan tarihi na Frankfurt an shigo da su ne ta hanyar da ta dace.
Musayar dadaddun al'adu
Gumakan al'adar yankin Nok an adana su ne a gidan tarihin na birnin Frankfurt a dakunan da aka ajiye kayan dadaddun al'adun Romawa da Girka da kuma Masar da su ma suka samo asali tun sama da shekaru 2000. A tare da su akwai sauran kayan tarihi daga al'adun wadannan kasashe. An kuma yi hakan ne domin kada wannan al'ada ta yankin Kudu da Saharar Afirka da ta kwashe tsawon shekaru ta bace.
Baje kolin kayan tarihi na farko
Baje kolin kayan tarihin da aka yi a Frankfurt shi ne irinsa na farko a nan Jamus da aka baje kolin kayan al'adun Afirka masu dadadden tarihi. Sama da gumaka da sauran kayan tarihi 100 ne aka gano a tsawon shekaru takwas da masana ilimin karkashin kasa na Jamus da Najeriya suka kwashe suna aiki a kai. Da wannan baje kolin da aka yi, an dora danbar yin bincike kan al'adar yankin Nok.