1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: 'Yan sanda 3 sun mutu a harin Goube

Ramatu Garba Baba
March 14, 2018

Ma'aikatar tsaron kasar Nijar, ta ce wasu jami'an 'yan sanda uku sun mutu a sanadiyar wani hari da mayakan jihadi suka kai a ofishin su da ke a garin Goube mai tazarar kilomita arba'in daga birnin Yamai.

https://p.dw.com/p/2uHWG
Nigeria Soldaten Archiv 2013
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Sanarwar ma'aikatar ta kara da cewa, wasu jami'a 'yan sandan sun sami rauni a dalilin harin na shekaranjiya Litinin. Garin na Goube mai tazarar kilomita arba'in daga Yamai babban birnin kasar ya kasance wani yankin da ke fuskantar hare-hare daga kungiyoyi na masu tayar da kayar baya a shekarun baya-bayan nan.

Wata kafar yada labarai a kasar ta bayar da labarin harin inda ta ce an kwashi tsawon mintuna talatin ana musayar wuta a tsakanin mayakan da 'yan sanda kafin daga bisani maharan su tsere bayan da wata rundunar tsaro ta kai doki ofishin. Ana dai kyauta zaton maharan da suka kai wannan harin sun fito ne daga kasar Mali da ke makwabtaka da Nijar.