Nijar: 'Yan adawa za su shiga majalisa
April 18, 2016A karshen mako ne dai 'yan adawa da ke karkashin kungiyar nan ta COPA suka bada sanarwa ta shiga majalisar dokokin kasar domin a yi aiki tare da su sabanin matakin da suka dauka a baya na cewar ba su shiga dukannin wata sabga ta majalisar ba saboda a cewarsu zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar da aka yi a watannin baya ba sahihi ba ne.
Baya ga batun shiga majalisar, a hannu guda kungiyar ta COPA ta kuma umarci wakilanta da ke aiki a hukumar zaben kasar ta CENI da su koma baki aiki domin halartar zaben kananan hukumomi da za a yi nan gaba. Abubakar Yakubu Maiga da ke zaman jigo a kungyar ta COPA ya ce umarnin da suka bada na 'ya'yansu su koma majalisa ba wai ya na nufin sun amince da halarci gwamnatin kasar ba, yunkuri ne kawai suke na yi wa kasa aiki.
Tuni dai al'umma a Nijar din suka fara bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta dangane da wannan matsayin da 'yan adawan suka dauka. Da dama daga cikinsu dai na cewar ba su ji dadin wannan matakin ba duba da yadda suka yi ta fafutuka tare da su wajen ganin cewar an daidaita al'amura a fagen siyasar kasar.
Yayin da magoya bayan 'yan COPA din ke nuna damuwa, wasu daga cikinsu na ganin tunda sun rigaya sun dau wannan mataki, ba su da wani zabi illa su goya musu baya domin suna da yakinin cewar dalilin daukar matakin na da karfin gaske duba da irin kwarewar da jagororin nasu ke da shi a fagen siyasa.