1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Takaddama tsakanin gwamnati da kungiyoyin farar hula

Mahaman Kanta MNA
March 26, 2018

Sabuwar dokar kasafin kudi a Nijar na ci-gaba da kawo kace-nace tsakanin gwamnati da kungiyoyin farar hula, har ta kai ga tsare wasu shugabannin farar hula.

https://p.dw.com/p/2v0pk
Niger Protest gegen das Haushaltsgesetz der Regierung
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A Jamhuriyar Nijar a wani yankurin zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar kasafin kudi da kungiyoyin farar hula suka so yi a ranar Lahadi, wadda hukumomi suka haramta musu, ya tada wata sabuwar takaddama a kasar, inda ake ci-gaba da tsare shugabannin kungiyoyin a ofishin 'yan sanda.

Wannan ya biyo bayan kone-konen tayoyi da wasu matasa suka yi, inda 'yan sanda suka tarwatsa su. Hakan ta sa 'yan sandar suka shiga kame shugabannin farar hular da suka shirya gudanar da zanga-zangar. Daga ciki wadanda aka tsare akwai Moussa Tchangari, shugaban Alternative Espace Citoyen, da Malam Nouhu Arzika, Shugaban MPCR, da Ali Idrissa, shugaban ROTAB  da kuma wani lauya mai zaman kanshi.

Niger Protest gegen das Haushaltsgesetz der Regierung
An samu kone-konen tayoyi a zanga-zangar da aka yi a bayaHoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Daurin kai kan lokacin yin zanga-zangar

A bangarensu hukumomi sun da da dalilin haramta zanga-zangar kamar yadda gwamnan jihar Yamai mai barin gado Seydou Zataou ya yi karin haske:

"Sun jima suna zanga-zanga. Kowane lokaci in sun tambaya ana ba su izini, amma ana yi musu kashedin da a yi zanga-zangar cikin kwanciyar hankali. Dalilin da ya sa aka hanasu a wannan lokaci shi ne wani sabon salo da suka sa. A cikin takardar da suka rubuta suka ce daga karfe hudu na La'asar zuwa har zuwa karfe 12 na dare. Wa ya taba jin an yi zanga-zanga a cikin dare? Ba yadda jami'an tsaro za su iya daukar alkawari na ba da kariya a wannan lokaci. Dalili ke nan da ya sa muka haramta wannan zanga-zanga."

Goyon baya daga 'yan adawa

Niger Protest gegen das Haushaltsgesetz der Regierung
Dubban mutane ne suka halarci gangamin da aka yi a watan FabarairuHoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Su ma a nasu bangaren 'yan siyasa na bangaren adawa da suka kira magoya bayansu da su halarci zanga-zangar sun yi tsokaci. Alhassane Intinikar shugaban jam'iyyar PNDP ya ce babu hujjar haramta zanga-zangar.

"In dai da gaske ne matsalar tsaro ta sa aka hana a yi jerin gwano, to matsalar tsaron sai ta hana a babban taro na PNDS Tarayya. Maganar da suka yi ba gaskiya ba ce. Saboda haka muka fito mu kama ma kungiyoyin farar hula, mu kama ma kasarmu mu fid da ita daga cikin kunci da wahala da take ciki, mu kuma yaki dokar kasafin kudi ta shekarar 2018."

Kungiyoyin farar hular sun ce wadannan kame-kame ba za su su yi kasa gwiwa ba, za su ci-gaba da gwagwarmaya har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.