Bankin Duniya: Arzikin Nijar ya karu
March 15, 2021Rahoton wanda Bankin Duniyar ya fitar a karshen mako, ya nunar da cewa tattalin arzikin Nijar ya karu da kaso shida da digo uku cikin 100, yayin da kowane dan Nijar ke samun kudin da ya kai na dalar Amirka dubu 555.
Karin Bayani: IMF ta ce tattalin arzikin Nijar ya bunkasa
Bankin Duniyar ya ce baya ga tashi daga matsayin mafi koma bayan kasashe da take rike da shi a fannin tattalin arziki shekaru da dama, a yanzu ta tsere wa kasashe kimanin 10 da suka hada da Saliyo wacce ta maye gurbin da Nijar din ta bari da Madagaska da Mali da Somaliya da Malawi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango da Laberiya da Mozambik da kuma Burundi.
Sai dai Malam Nasiru Seidu na kungiyar Muryar Talaka a Nijar, na ganin wadannan alkaluma na Bankin duniyar sun saba wa zahirin abin da dan Nijar ke gani a kasa.
Karin Bayani: Zaman taron hukumar CESOC a Nijar
Amma kuma a daidai loakcin da wasu 'yan Nijar din ke musanta ci-gaban da Bankin Duniyar ya ce kasar ta samu a fannin tattalin arziki, Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen, na ganin abin alfahari ne domin kuwa gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou ta aiwatar da ayyukan da suka dora Jamhuriyar ta Nijar a kan turbar ci-gaba. Kawo yanzu dai gwamnatin Jamhuriyar Nijar din ba ta ce komai ba game da wannan rahoto na Bankin Duniya, wanda ke ci gaba da haifar da muhawara a tsakanin al'ummar kasar dangane da ingancinsa ko akasin haka.