Zargin hana sojojin Nijar jawabi a taron New York
September 23, 2023A sanarwa da aka fidda a gidan talbijin na kasa, sojojin Nijar sun ce Antonio Guterres ya kauce hanya wajen gudanar da aikinsa inda ya hana Nijar yancinta na halarta taron karo na 78, suna masu cewa hakan ka iya kawo cikas a kokari na kawo karshen rikicin da suke fama da shi a kasarsu. Kazalika sanarwar ta caccaki shugaban na MDD da yaudara.
Karin bayani: Cece-kuce kan Jamhuriyar Nijar a Majalisar Dinkin Duniya
A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne dai sojoji a jamhuriyar Nijar suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum, wanda har kawo yanzu suke ci gaba da tsare shi da iyalansa.
Kasashen duniya da manyan kuungiyoyi a ciki da wajen nahiyar Afirka har da Majalisar Dinkin Duniya sun yi mummunar suka kan kifar da halastacciyar gwamnatin farar hula.
Yunkurin samun mafita a rikicin shugabancin Nijar din na ci gaba da fuskantar kalubale, tsakanin sojojin da kuma kungiyar Ecowasda ta umurci su mayar da shugaba Bazoum a kan mulkinsa, inda su kuma a nasu bangare suka ce za su mika mulki ne kawai bayan sun yi shekaru biyu a kan madafun iko.