Mahamadou Issoufou na neman taka wa Hama Amadou birki
August 14, 2019Talla
A Jamhuriyar Nijar wata hira da Shugaban Kasar Issoufou Mahamdou ya yi da wata jarida ta haifar da muhawara musamman ma inda kusan a karon farko ya yi magana kan babban mai adawa da shi Hama Amadou. Wanda a halin yanzu yake gudun hijira a Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Nijar. A tattaunawar da aka yi da shi, ya jaddada matsayinsa na neman a taso masa keyar Hama Amadou zuwa Nijar ko kuma a nesantar da shi daga kasar ta Benin. Lamarin da ake ganin tamkar babu wata alama ta yin sulhu tsakanin wadanda a baya suka kasance abokan juna.