1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya sheka tsakanin 'yan siyasa a Nijar

Salissou Boukari MNA
April 30, 2019

A Jamhuriyar Nijar batun ficewa daga wannan jam'iyya zuwa wata ko kuma korar 'yan siyasa masu mukamin 'yan majalisa daga cikin jam'iyya na ci gaba da kasancewa ruwan dare gama duniya a jam'iyyu da dama na kasar.

https://p.dw.com/p/3HiHl
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Na baya-bayan nan shi ne na jam'iyyar UDR Tabbat ta tsohon Firaminista Amadou Boubakar Cisse wadda ta kori wasu 'yan majalisa biyu daga cikinta.

A baya dai an samu jam'iyyu irin su MPN Kishin Kasa ko ANDP Zaman Lafiya zuwa su jam'iyyar Amine-Amine ta Ladan Chana, da suma suka fuskanci irin wannan matsala tare da 'yan majalisar dokokinsu sakamakon abin da ake zarginsu da shi na kin bin umarnin uwar jam'iyya.

Wannan matsala dai ta zo ga jam'iyyar UDR Tabbat ta tsohon Firaminista Amadou Boubakar Cisse, inda ta sanya mata daukan mataki na korar wasu 'yan majalisar dokokinta biyu daga jam'iyyar sakamakon abin da aka kira kin bin umarnin jam'iyya da suke yi.

Sai dai daga bangaren wadanda aka korat ta bakin Honorable Yakouba Soumana wannan mataki sun yi maraba da shi ganin cewa sun jima suna jiran jam'iyyar ta koresu domin a cewarsu tun daga shekara ta 2016 ba su da labarin shugaban jam'iyyar ta su Amadou Boubakar Cisse.

Sai dai a cewar dan majalisa Soumaila Ali na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki, wannan matsala ta tsakanin 'yan majalisa da uwar jam'iyyarsu an jima ana samunta, amma a wannan karo ta fi kamari, inda ya ce kuma babban dalilin da ke haifar da ita, shi ne na rashin hakuri.

Tuni wasu suke zargin jam'iyya mai mulki da laifin haddasa wannan matsala a cikin jam'iyyu domin raba 'yan majalisa da jam'iyyun nasu, zargin da dan majalisa Soumaila Ali ya karata, inda ya ce ko wane dan majalisa dattijon kansa ne don haka babu zancen cewa jam'iyya mai mulki za ta hure masa kunne har ya dawo daga rakiyar jam'iyyarsa.