An sake dage shari'ar Moussa Aksar
March 26, 2021A wannan Jumma'a ya kamata a ci gaba da sauraron shari'ar, sai dai tilas aka dage zaman kasancewar mutuman da ya shigar da karar bai halarci zaman kotun ba. Barisata Boudal Mouloud Effred na zaman guda daga cikin lauyoyin da ke kare dan jaridar Moussa Aksar ya kuma shaidawa manema labarai cewa, alkali ya daga shari'ar zuwa ranar biyu ga watan Afrilu mai zuwa.
Karin Bayani: Bincike kan badakalar makamai a Nijar
Wannan dai shi ne karo na uku da ake dage wannan zaman shari'a ta badakalar kudin makamai, inda wani dan Nijar mazaunin kasar Beljiyam, ya kalubalanci dan jaridar mai binciken kwakwaf a gaban kuliya bisa zargin cewa dan jaridar yi masa sharri. Lokacin fitowarsa daga kotun Malam Moussa Aksar ya yi tsokaci a gaban ‘yan jarida yana mai nuna kwarin gwiwa a game da wannan shari'a.
A ranar 20 ga watan Satumbar bara ne dai, dan jaridar Moussa Aksar ya wallafa wani rahoton binciken da ya yi da wasu kungiyoyin yaki da yaduwar kudin haram na kasa, inda ya bankado wannan badakala ta cuwa-cuwar da wasu shafaffu da mai na kusa da gwamnati suka yi a wajen cinikin makamai da gwamnati ta nemi sayowa sojojin kasar domin yakar ‘yan ta'adda da kuma yadda suka karkatar da akalar kudin zuwa aljifansu.
Karin Bayani: Suka kan tsare 'yan farar hula a Nijar
Tuni dai kungiyoyin fararan hula suka fara nuna damuwarsu da yadda zaman shari'ar ya faskara har ya zuwa yanzu, inda suke ganin da akwai lauje cikin nadi. Yanzu dai jama'a sun zura ido su gani, ko zaman shari'ar da aka dage zuwa ranar biyu ga watan goben zai wakana ko kuma za a sake daga wa.