Nijar: Sabbin dokoki kan 'yan ta'adda
May 30, 2024Gwamnatin ta dauki matakin samar da sabbin dokokin kula da tubabun 'yan ta'addan a kokarin da take na shawo kan matsalar ayyukan ta'addanci a kasar daura da matakan soja da ta ke dauka.
A shekara ta 2019 ne a karon farko a wani mataki na yaki da ayyukan ta'addanci da suka mamaye wasu yankunan kasar, Nijar ta soma fito da wannan tsari na karbar tubabbun 'yan ta'adda domin basu wata dama ta komawa rayuwa mai tsafta a tsakanin al'umma. Sai dai ganin irin yadda adadin 'yan ta'adda da 'yan tawaye da sauran 'yan bindiga ke nuna sha'awar aiyje makamansu da kuma tuba daga muggan ayyukan nasu, Nijar ta dukufa samar da sabbin dokoki wadanda za su ba ta damar tafiyar da aiki a cikin nasarar fiye da a baya kamar dai yadda Malam Ibrahim Malam Goni babban jami'in kula da makomar tubabbu 'yan ta'adda a ma'aikatar cikin gida ta Nijar ya baiyana.
Taron tsara sabbin dokokin tafiyar da aikin kula da tubabbun 'yan ta'addan ya samu halartar wakilan gwamnati da na kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin cikin gida masu zaman kansu. .
Hukumar Raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya na a sahun gaban kungiyoyin da ke tallafa wa shirin na samar da sabuwar makoma ga tubabun 'yan ta'addan. Kuma jagorar kungiyar ta UNDP a Nijar Madam Nicole Koissi ta ce a shirye suke su ci gaba da taimaka wa gwamnatin a cikin wannan aiki.
Daga shekara ta 2016 zuwa yanzu 'yan ta'adda sama da dubu daya da 600 ne daga Jihohin Diffa da Tillabery da Tahoua suka tuba tare da mika wuya ga hukumomi tare da samun horo a cibiyoyin Goudoumariya da Hamdallahi, shirin da yanzu gwamnatin ta Nijar ke son fadadawa a karkashin sabbin dokokin da za su samar a nan gaba a karkashin wani kwamiti na musamman.