Siyasar Nijar cikin halin ni tasku
February 11, 2021Talla
Tuni dai kungiyoyin fararen hula da ke fafutukar kare dimukuradiyya a Jamhuriyar ta Nijar, suka fara fitowa fili suna yin tir da yadda wasu al'ummar kasar da ma 'yan siyasa ke furta kalaman da ke da nasaba da kabilanci da bangaranci.
Yakin neman zaben da ke tattare da rikici da kasar ta samu kanta a ciki dai, na neman saka siyasar Jamhuriyar ta Nijar cikin halin rashin tabbas. A halin yanzu dai 'yan takarar neman shugabancin kasar da masu mara musu baya, na ci gaba da furta kalamai iri-iri a gaban dumbun magoya bayansu, inda a wasu lokutan su kan zarme su furta kalaman da ba su dace ba.