Raguwar mutuwar aure a birnin Yamai
January 10, 2023A kowacce shekara babbar kungiyar addinin Muslumci ta Jamhuriyar Nijar din ko AIN a takaice da ke gudanar da shari'a kan rigingimun aure da na gado da sauran matsaloli na zamantakewa, na fitar da rahoto kan yawan mace-macen auren da aka fuskanta a birnin na Yamai. Kungiyar ta AIN ta ce wani abin farin ciki shi ne a shekarar da ta gabata mutuwar auren ta ragu a birnin Yamai, birnin da ya yi kaurin suna wajen mace-macen auren da wasunsu ma ba a wuce mako guda bayan daurawa. Kungiyar taAIN ta ce karairayi da ma'auratan ke yi wa juna ko auren jari da wasu ke yi da kuma rikicin binciken salula, na daga cikin dalilan da ke haddasa mutuwar aure a wannan zamanin. Tuni dai kungiyar SOS Femme et Enfant Victimes de Violance Familiale da ke fafutukar kare hakkin mata da yara a kasar, ta bakin shugabarta Mme Ahmed Mariama Moussa ta bayyana gamsuwarta da wannan ci gaba da aka fara samu a zamantakewar aure a Nijar din. Kungiyar ta AIN dai ta ce akwai dubban aurarrakin da ta ceto a birnin na Yamai a shekarar ta 2022, kuma ta dauki sababbin matakai na ganin adadin auren da ke mutuwa ya ragu a wannan shekara ta 2023 da muka shiga.