Nijar: Neman sakin dan Amirka da aka sace
October 15, 2017Mutanen na garin na Abalak da ke a nisan km 350 Arewa maso gabashin birnin Yamai, sun ce wadanda suka dauke Jeffery Woodke ba wai dan kasar Amirka suka dauka ba sun dauke dan garin Abalak ne kamar yadda suka sanar a gaban sarakuna da sauran magabatan yankin na Abalak. Shi dai Jeffery Woodke ma'aikacin agaji dan kasar Amirka an dauke shi ne a daren 14 ga watan Octoba na 2016 a cikin gidansa da ke birnin na Abalak wanda sace shi ya yi sanadiyyar mutuwar mutun biyu da suka hada da jami'in tsaro daya da kuma wani farar hulla. Al'ummar ta Abalak sun ce suna masu tunawa ga iyallan Jeffery musamman ma matarsa da 'ya'yansa biyu, inda suka ce tuni sun rubuta shi a cikin jerin sunayen gwarzayensu na Abalak. Shi Ba'amirken ya kasance ya na aiki tare da wata kungiyar mai zaman kanta a garin na Abalak tun daga 1992 kuma ya na rayuwa tamkar dan kasar Nijar.