Matakan kariya bayan gobara a maradi
November 11, 2021Za dai a iya cewa daukar wannan mataki ya zama tilas, bayan da a karo na biyu gobara ta lakume rayukan yarar kanana a jihar Maradi. A baya dai gobarar ta lakume rayukan yara kanana da ke makarantar reno ko kuma share fagen shiga firamare a Yamai fadar gwamnatin kasar.
Ana dai alakanta yawaitar afkuwar haduran gobara a irin wadannan makarantu da yadda azuzuwan suka kasance na zana maimakon ginin bulo ko kasa, abin da ya sanya mahukuntan na Nijar daukar matakin hana sanya kananan yara a irin wadannan azuzuwa da ke bangaren renon na makarantun firamaren kasar.
Mutuwar daliban makarantar firamaren ta Maradi da shekarunsu suka kama daga bakwai da kuma suke daukar darasi a guda daga cikin makarantun renon da aka mayar firamare dai, ya daga hankulan al'umma tare da sanya al'hini a cikin da wajen kasar.