Nijar: Martani kan daure Baba Alpha
July 20, 2017Kotun cikin hukuncin na ta ta ce ta janye masa duk wani 'yancinsa na zama dan kasar Nijar bisa zarginsa da yin takardar zama dan kasa ta jabu. Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce dan jaridar Baba Alpha mutun ne da aka san shi da sukar lamurran gwamnatin ta Nijar inda ta yi Allah wadai da launi na siyasa da aka bai wa wannan kamu na shi sannan ta ce wannan hukunci ya yi tsananin gaske wanda kuma burin shi ne na toshe bakin dan jaridan tare da hana masa ayyukan da yake yi na fadin gaskiya komin dacinta, inda ta yi kira ga hukumomin na Nijar da su dawo kan bakansu na wannan hukunci.
Lawyan da ke kare Baba Alpha Barista Boubakar Mossi ya tabbatar cewa dan jaridan an haife shi a Nijar kuma ya girma a Nijar sannan ya auri 'yar Nijar har suna da 'yan'ya biyu, yayin da shi kan shi dan jaridar ya sanar cewa mahaifinsa ya share shekaru 45 a cikin kasar Nijar.