1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar jam'iyyar Lumana bayan taruka biyu a Yamai da Dosso

Salissou Boukari MNA
August 5, 2019

Bangarori biyu da ke hamayya da juna a jam'iyyar Lumana Afirka sun shirya taro biyu a Dosso da kuma Yamai, sai dukkansu biyu sun goyi baayan tsayar da Hama Amadou takara.

https://p.dw.com/p/3NMzN
Niger Sitz der Fraktion der Oppositionspartei Moden Fa Lumana
Hoto: DW/D. Köpp

Ranar hudu ga watan Augusta 2019 ta kasance rana mai cike da tarihi ga 'yan jam'iyyar Lumana Afirka ta Hama Amadou da ke a matsayin babbar jam'iyya ta adawa a Jamhuriyar Nijar, wadda ta wayi gari da babban taron Congres har biyu, inda kuma dukanninsu suka zabi shugaban jam'iyyar a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar takara a zabe mai zuwa.

Ganin cewa bangaran Oumarou Noma da ke buga gaba da wata takardar kotu da ya samu wadda ta soke tsigewar da aka yi mishi daga shugaban riko na jam'iyyar, da kuma bangare daya na jam'iyyar da

ke da goyon bayan kusan dukkannin mambobin kwamitin zartaswarta, da shugaban jam'iyyar Hama Amadou, da 'yan majalisa na jam'iyyar, da ma samun halartar shugabannin jam'iyyun adawa a wurin taron na Yamai, sanya ayar tambaya kan bangaren da zai samu halascin tafiyar da harkokin jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar adawa ta Lumana Hama Amadou da ke gudun hijira a kasar waje
Shugaban jam'iyyar adawa ta Lumana Hama Amadou da ke gudun hijira a kasar wajeHoto: DW/S. Boukari

A jawabin da ya yi ta faifayen bidiyo ga babban taron na Yamai uban jam'iyyar ta Lumana, Hama Amadou da ke gudun hijira a kasar waje, ya jaddada goyon bayanshi ga 'yan jam'iyyar da ya ce suka jure wa duk wani salo na jan ra'ayinsu daga bangaren masu mulki, inda ya ce dokokin jam'iyyar Lumana dai ba su bai wa ko shugaban jam'iyyar izinin shirya taro ba tare da amintar kwamitin zartaswa ba.

Taron na Yamai a mataki da ya dauka mai lamba tara ya ce tamkar Oumarou Noma ya fitar da kanshi daga jam'iyyar da ma dukkannin wadanda suka je Dosso domin gudanar da taron jam'iyyar sabanin wanda kwamitin zartaswa da ke da goyon bayan Hama Amadou ya yi a Yamai.

A yanzu dai da bangaren Oumarou Noma da kuma bangaren kwamitin zartaswa na Lumana da ke da goyon bayan Hama Amadou, dukkanninsu za su zuba idanu domin ganin wanda kotu zai bai wa gaskiya dangane da babban taron da ya gudana, sannan ko bangaran da ya sha kaye zai rungumi kaddara ko kuma za a buda wata doguwar tafiya ce ta shari'a a cikin jam'iyyar? Wannan ayar tambaya ce da sai nan gaba za a samu amsarta.