1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kotu ta cire wa Bazoum rigar kariya

Gazali Abdou Tasawa
June 14, 2024

A Jamhuriyar babbar kotun kasar ta Cour d'Etat ta cire wa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum rigar kariya a wani zama da ta gudanar a birnin Yamai ba tare da gabatar da shi a gaban kotun ba.

https://p.dw.com/p/4h3VB
Hambararren shugaban kasa Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren shugaban kasa Nijar Mohamed Bazoum Hoto: Boureima Hama/AFP/AP/dpa/picture allaince

Hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar ne suka shigar da wannan bukata a gaban babbar kotun ta kasa domin samun damar gurfanar da hambararren shugaban a gaban kuliya a kan wasu jerin zarge-zarge da suke yi masa da suka hada da laifin cin amanar kasar. Sai dai a yayin da wasu ‘yan Nijar ke nuna farin cikinsu da matakin kotun wasu na ganin allura na iya tono garma a shari'ar da za a yi wa hambararren shugaban kasar.

Ba dai tare da wani bata lokaci ba ne a zaman nata da ta yi a wannan Juma'a a birnin Yamai babbar kotun kasar ta Nijar ta sanar da cire wa hambararren shugaban kasar Bazoum Mohamed rigar kariya kamar yadda hukumomin mulkin sojan suka nema. Jim kadan bayan bayyana hukuncin Maitre Salim Ould Said daya daga cikin lauyiyin Bazoum ya yi wa manema labarai tsokaci a kai yana mai cewa:

”Kamar yadda kuka gani a nan tare da mu, yau kotu ta dauki mataki da ta cire rigar kariya ga Shugaba Bazoum. Kun san tambayoyi biyu aka gabatar a gaban kotun. A kwai alkalin da ya ce yana so a daga kariyar shugaban kasa dan ya tuhume shi, shi wannan bukata an yi watsi da ita. Tambaya ta babban mai shigar da kara na gwamnati ne ya shigar da ita. Ita kotu ta amince da ita sun dage kariyar shugaban kasa Mohamed Bazoum. Wannan na nufin cewa a yanzu an cire masa rigar kariya suna iya gurfanar da shi. To shi ne na ce a nan gaba illahirin lauyoyin Bazoum za mu yi taro mu yi shawara daga karshe zam u fitar da sanarwa a kan batun"

Tarin ‘yan kallo ne dai magoya baya da kuma masu adawa da hambararren shugaban kasar suka halarci zaman shari'ar cire rigar kariya. 

Sai dai wasu daga cikin magoya hambararren shugaban kasar sun bayyana fatan ganin sharI'ar da za a yi masa a nan gaba bayan cire masa rigar kariya ta kasance a bainal jama'a ta yadda ‘yan kasa za su fahimci dalilan kabli da na ba'adi na juyin mulkin da aka yi masa da kuma laifukan da sojojin ke zarginsa da aikatawa.

Hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar na zargin hambararren shugabararren shugaban kasar ne da aikata laifuka da suka kira ga a kawo wa Nijar hari domin kwatar shi daga hannu sojojin da suka kifar da shi don mayar da shi a kan kujerarsa, da kuma ma zargin yi wa harkokin tsaron kasa zagon kasa da dai wasu laifukan na daban da suka hada da cin amanar kasa.  Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga ranar da hukumomin mulkin sojan za su gurfanar da hambararren shugaban kasar a gaban kotu.