1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Jerin gwanon kungiyoyin farar hula

Salissou Boukari
December 21, 2016

Da yammacin wannan rana ta Laraba hadin gwiwar kungiyoyin fararan hula da 'yan siyasa suka gudanar da wani jerin gwano na lumana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/2UglU
Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

Masu zanga-zangar sun zargi hukumomin Nijar da yin halin ko in kula da tabarbarewar lamura a kasar masamman harkokin ilimi, sannan ga karayar tattalin arziki, da kuma rishin hukunta wasu wadanda ake zargi da aikata laifuka a kasar. Masu jerin gwanon dai sun soma ne daga wani fili da ake kira "Place Toumo" da ke birnin Yamai har zuwa harabar majalisar dokoki da ake kira "Place da la concertation", inda wadanda suka shirya zanga-zangar suka gabatar da kokensu tare da sukar lamirin hukumomin na Nijar, musamman Shugaban kasar Issoufou Mahamadou da suke cewa ya kasa.

Sai dai yayin wani jawabi da ya yi albarkacin zagayowar cikon shekara ta 58 da kasar ta zamanto Jamhuriyya, shugaban na Nijar ya sha alwashin kawo sauye-sauye domin inganta tattalin arzikin kasar a shekara mai kamawa ta 2017.