Sabon harin 'yan ta'adda a Nijar
November 4, 2021Talla
A cewar majiya daga al'ummar yankin ta bakin wani dan majalisa da ke wakiltar yankin Tillaberi dai, mutane sama da 80 ne aka kashe. Rahotanni sun nunatr da cewa wasua mutanen tara sun yi batan dabo kana wasu 15 suka samu nasarar tserewa a yayin hare-haren da aka kai a ranar Talatar wannan makon. Wata majiya daga yankin ta nunar da cewa, magajin garin na Banibangou na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin hare-hare.