1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsuwar kama aikin Bazoum a Nijar

April 2, 2021

Bazoum Mohamed ya zama sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar bayan kammala wa'adin shekaru 10 na tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou. Karon farko da gwamnatin farar hula ta mika mulki ga wata a Jamhuriyar ta Nijar.

https://p.dw.com/p/3rWtd
Niger Präsident Bazoum
Hoto: Gazali A. Tassawa/DW

A yau ne aka rantsar da sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar, bayan cikar wa'adi biyu na shekaru 10 da tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya kwashe ya na jagorancin kasar. Bazoum Mohamed ya zama zababben shugaban kasa bayan da kotun tsarin mulki ta tabbatar masa da nasara, a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Bikin shan ratsuwar dai ya samu halartar shugabannin kasashe dabam-dabam na duniya da kuma jami'an diplomasiyya na ciki da wajen kasar. Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar, inda wata gwamnatin farar hula ta mika mulki ga wata gwamnati ta farar hula.