1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin cire wa Bazoum rigar kariya

Gazali Abdou Tasawa
April 5, 2024

Babbar kotun koli ta kasa a Nijar ta yi zama domin cire rigar kariya ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum wanda hukumomin mulkin sojan ke son gurfanarwa a gaban kuliya.

https://p.dw.com/p/4eUG4
Hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed BazoumHoto: Evelyn Hockstein/Pool/File Photo/REUTERS

Babbar kotun kolin Nijar mai alkalai 23 ta dukufa wajen duba takardun da gwamnatin kasar ta Nijar ta shigar a gaban kotun tana mai bukatar kotun ta cire  wa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum rigar kariya da doka ta ba shi, aikin da ke zama matakin farko da zai bai wa gwamnatin mulkin sojan kasar damar gurfanar da hambararren shugaban kasa a gaban kuliya bisa zarginsa da aikata laifuka da dama da suka hada da na cin amanar kasa.

Maitre Moussa Coulibaly daya daga cikin lauyoyin hambararren shugaban kasar wanda ya samu halartar zaman kotun ya bayyana cewa ya yi kokarin ganin kotun ta daga zaman shari'ar kasancewar ba a ba shi damar ganin takardun karar ba domin sanin abin da suka kunsa, kuma ba a ba shi dama ganawa ko tattaunawa da hambararren shugaban kasar da yake karewa ba.

Jamhuriyar Nijar | Mohammed Bazoum | Kotu | Rigar Kariya
Kotu na shirin cire Bazoum rigar kariya ga BazoumHoto: DW/M. Kanta

Sai dai mataki na cire rigar kariya ga hambararren shugaban aksa ya soma haifar da mahawara a tsakanin ‚yan kasar kan dacewarsa ko akasin haka. A karshen zamanta na wuni daya, kotun ta tsaida ranar 10 ga watan Mayu na 2024 a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncin nata a kan bukatar hukumomin mulkin sojan kasar na cire rigar kariya ga hambararren shugaban kasar domin gurfanar da shi a gaban kuliya.