1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An kashe ma'aikatan kamfanin Foraco

Ahmed Salisu
November 22, 2018

Rahotanni daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar na cewar wasu mutane sun hallaka wasu ma'aikatan kamfanin Foraco na kasar Faransa wanda yanzu haka ke aiki na gina wasu rijiyoyi a Diffa din.

https://p.dw.com/p/38idS
Niger Flagge

Wata sanarwa da kamafnin ya fidda dazu ta ce da misalin karfe biyu na daren jiya Laraba ne mutanen suka afka inda ma'aikatan kamfanin na Foraco ke kwance suka hallaka bakwai daga cikinsu da kuma wani farar hula guda.

Baya ga wanda suka rasu din, kamfanin ya ce wasu karin mutane biyar sun jikkata kuma biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali. Wani jami'in tsaro da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters kuma ya zabi a sakaya sunansa ya ce kila maharan 'yan kungiyar nan ta ce Boko Haram.

Ya zuwa yanzu kungiyar ba ta dau alhakin kai wannan hari ba, sai dai a baya ta sha kai jerin hare-hare a yankin na Diffa da ke makotaka da Najeriya inda ta hallaka mutane da dama.