Nijar: Ambaliyar ruwan ta yi kamari a birnin Yamai
August 27, 2017Talla
Gwamnan ya yi wannan kira ne bayan wasu ruwa masu karfin gaske da suka sauka a ranar Asabar a birnin na Yamai suka haddasa babbar ambaliyar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutun biyu, bayan da dakin da suke ciki ya fada musu. Shi ma dai daga na shi bangare babban darektan ma'aikatar agajin gaggawa ta kasa Abdoulaye Bako, ya jaddada wannan kira ga jama'a da su fice daga yankunan da duk ake fuskantar barazanar ambaliya, musamman ma yankin Guntu-Yena da ke a matsayin wata tsofuwar hanyar ruwa da a yanzu ruwa suka sake komowa a gareta, da kuma unguwar Gabagoura. Gidaje fiye da 300 suka ruguje a cewar mazauna unguwar. Daga watan Yuni kawo yanzu dai ambaliyar ruwan saman ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 a kasar ta Nijar.