1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani bangaren rikicin Libiya ya nemi sasantawa

Binta Aliyu Zurmi SB
June 6, 2020

Jagoran yakin kasar Libiya Khalifa Haftar wanda yake rike da gabashin kasar ya amince tsagaita wuta tare da neman ganin sasantawa.

https://p.dw.com/p/3dMBt
Libyen-Ägypten-Waffenruhe
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Biyo bayan nasarar da suka samu a jerin hare-haren da dakarun sojin Libiya masu biyayya ga gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ya zuwa yanzu dai Jagoran yaki da ke rike da gabashin kasar Khalifa Haftar ya amince da yarjejeniniyar tsagaita wuta da aka cimma a Alkahirar Masar.

Yarjejeniyar da Shugaba Abdel Fatah al-Sisi na Masar ya bayar da sanarwar kulla ta, za ta fara aiki ne a ranar Litinin mai zuwa 8 ga watan nan da muke ciki na Yuni.

Sanarwar na zuwa ne yayin da dakarun gwamnatin hadin gwiwa suke zafafa kai hare-hare da nufin sake kwato garin Sirte wanda shi ne mahaifar hambararen shugaban kasar Maragayi Muammar Ghaddafi, sai dai da alama mai magana da yawun dakarun gwamnatin Mohamad Gnounou na kokarin shashantar da yarjejeniyar inda ya ce su ne ke da zabin lokacin da za a kawo karshen yakin.