Nelson Mandela na fama da rashin lafiya
February 25, 2012Wata sanarwa fadar gwamnatin ta ce shugaba Jacobe Zuma ya ce an riƙe Nelson Mandela saboda ya na fama da rashin lafiya wanda likitoci suka ce ya na buƙatar kulawa ta ƙwarraru.
Mandela wanda shi ne shugaban Afirka ta ƙudu na farko baƙar fata bayan faduwar gwamntin mulkin wariyar launin fatawanda kuma ya ke da shekaru 93 da haifuwa na fama da ciwon ciki kamar yadda sanarwa gwamnatin ta baiyana.To amma daga bisanin kuma wata jikanyar sa ta sanar da manema lanbarai cewar babu wani fargaba akan rashin lafiyar ta sa.A shekara bara hankula jamma'ar ƙasar ya kadu so sai sa'ilin da aka riƙe tshohon shugaban ƙasar a asibitimarabin Madiban da ya fito a benar jama'a tun a shekara ta 2010 lokacin da aka gudanar da gasar cin kofin duniya ta kwalon kafa a Afirka ta ƙudu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohamme Nasiru Awal