Nasarori a yaki da zazzabin cizon sauro
December 12, 2014Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokaci a kan ci-gaban da aka samu wajen yaki da zazzabin cizon sauro wato Malaria.
Jaridar ta fara ne da rawaito al'kalumman da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayar da ke nuna cewa daga farkon wannan karni zuwa yanzu rabin mutanen da suka kamu da Malaria, cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya. Sai dai jaridar ta ce yawansu ya kai mutu 1500 a kowace rana inda kusan dukkansu kananan yara ne akasari kuma a nahiyar Afirka. Sai dai daga shekarar 2000 zuwa ta 2013 nahiyar ta samu koma bayan kashi daya bisa hudu na wadanda suka kamu da Malaria, yayin da tsukin wannan lokaci nahiyar ta Afirka ta samu karuwar yawan al'umma na kimanin kashi 43 cikin 100. Wannan ci gaban ya samu ne saboda kwararan matakan da ake dauka na yaki da zazzabin cizon sauro. Jaridar ta ce duk da haka bisa ga dukkan alamu a Afirka, ba za a iya cimma burin da aka sa a gaba na rage yawan Malaria zuwa rabinsa na yanzu kafin shekarar 2015 ba.
Iyalin Mugabe sun mamaye siyasar Zimbabwe
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali ne a kan kasar Zimbabwe biyon bayan babban taron da jam'iyyar Zanu-PF mai jan ragamar mulki a kasar ta yi a makon da ya gabata inda ta sake zaben shugaban kasa Robert Mugabe a matsayin shugaban jam'iyyar, sannan matarsa Grace Mugabe a mukamin shugabar reshen mata na jam'iyyar.
Jaridar ta ce yanzu dai Grace Mugabe ta tsallake matakin farko a burinta na zama shugabar kasa. Ba a kai watanni uku ba da uwargidan Mugaben ta fito fili ta nuna sha'awarta na darewa kan wannan mukami, inda ta yi rangadi a fadin kasar. Sabanin mijinta mai shekaru 90, wanda kuma bisa ga alamu bai da cikakkiyar masaniya ga abubuwan da ke wakana a wajen fadarsa, ita Grace Mugabe 'yar shekaru 49 ta dukufa wajen gudanar ayyukan jin kai a kokarin wanke kanta. Yanzu haka ta gina wani gidan marayu a wajen birnin Harare, babban birnin kasar. Kuma tana da kyakkyawan dama. Domin Joice Mujuru da ke zama babbar 'yar hamaiyatarta kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa, tuni an yi waje da ita bayan Mugabe ya zarge ta da yunkurin hambarar da shi.
Mabambamtan ra'ayoyi game da hukuncin ICC
Bangare daya kadai ya gamsu inji jaridar Die Tageszeitung tana mai cewa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi matukar farin ciki bayan da kotun hukunta laifukan yaki da kasa da kasa ta yi watsi da shari'ar da ake masa na hannu a rikicin bayan zaben kasar ta Kenya a karshen shekarar 2007. To sai dai a cewar jaridar hukuncin ya janyo damuwa game da zaman lafiyar kasar. Ta ce kabilar Kikuyu da Kenyatta ya fito ciki, na ganin hukuncin a matsayin kwakkwarar shaidar cewa ba ya da laifi. Amma a tsakanin 'yan kabilar Kalenjin ta mataimakin shugaban kasa William Ruto ba haka abin yake ba, domin akwai shari'arsa a gaban kotun. A zaben shekarar 2013 mutanen biyu sun kulla kawance da nufin kyautata rayuwar al'ummar Kenya, amma masu sukar lamiri sun ce babban kawance ba komai ba ne illa dabarar kauce wa hukuncin kotun kasa da kasa.