1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Runduna ta musamman don kare makarantu

March 25, 2024

Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin kafa rundunar tsaro ta musamman don kare makarantu daga hare haren 'yan ta'adda

https://p.dw.com/p/4e6ig
Nigeria Gangs Gewalt Bürgerwehr Entführung
Hoto: AFP

A yayin da ake kallon karuwar ta’azzarar sace dalibai 'yan makaranta, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na shirin kafa wata runduna ta musamman da nufin kare makarantun kasar a nan gaba.

Kama daga 'yan matan Chibok zuwa 'yan Kuriga dai sau 15 ana shiga makarantu da sace dalibai a Najeriya.

Daruruwan makarantu ne dai yanzu haka ke fuskantar barazanar sace dalibai a cikinsu a sashen arewacin kasar da ke zaman na baya ga dangi. To sai dai kuma Abujar ta ce ta na shirin kafa wata runduna ta musamman da nufin kare makarantu kasar.

Wasu daga cikin 'yan makaranta Kuriga da aka 'yanto
Wasu daga cikin 'yan makaranta Kuriga da aka 'yanto Hoto: Ibrahim Yakubu/DW

Karin Bayani: An saki dukkan daliban Kuriga da aka sace a Najeriya

Tinubu dai a fadar sanarwar fadar gwamnatin kasar na neman hanyoyi na kwantar da hankula cikin makarantun da nufin samun damar karatu a natse.

Koma ya zuwa ina Abujar ke fatan kaiwa a cikin neman mafitar rikicin sace daliban makarantun dai, iya kai wa ga tsaron makarantun a fadar kabiru Adamu kwarararen masanin tsaro ana bukatar sake nazarin dabaru bisa makomar makarantun arewacin kasar.

Karin Bayani: Sojin Najeriya sun lashi takobin kubutar da daliban Kuriga

Tun daga satar 'yan matan Chibok a shekara ta 2014 mahukuntan Najeriyar ke fitar da dabarun neman samar dat saro a makarantun kasar.

Sojoji a shirin ba da kariya ga yan makaranta a Najeriya
Sojoji a shirin ba da kariya ga yan makaranta a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Dabarun kuma da daga dukkan alamu ke karewa cikin shiri ntakardu, maimakon kai wa ga kwantar da hankula cikin makarantun,

Sannu a hankali dai satar 'yan makaranta na dada jefa makomar ilimi a arewacin kasar cikin tsaka mai wahalar gaske.

Makarantu 800 ne dai yanzu haka ke a rufe a sashen arewacin kasar da ke kallon raguwar yaran da ke zuwa makaranta yanzu haka.