1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 20

January 6, 2020

Hukumomin Batsari da Jibiya a Katsina sun tabbatar da labarin yadda 'yan bindiga suka yi garkuwa da sama da mutum 20 a yayin da suke hanyar komawa gida bayan da suka dawo daga cin kasuwa.

https://p.dw.com/p/3Vm59
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Lamarin ya jefa al'umma cikin fargaba a yayin da al'ummar yankin da aka kai wa harin ke fama da zullumi, musamman wadanda aka sace wa dangi, illa kudaden da za su bayar na fansar 'yan uwansu da aka sace daga dajin Batsari. Ita kuwa jihar Zamfara da ke makwabtaka da jihar Katsina, bayan sasanci da ita ma tai da 'yan bindiga, ta sake samun kanta cikin yanayi na matsalar tsaro, rahotanni na nuni da cewa ana fuskantar hare-hare, don ko jiya an samu asarar rai a karamar hukumar Shinkafi. 

Dawowar wadannan hare-hare na neman maida hannun agogo baya a bangaren mahukunta da ke cewa suna kokarin magance matsalar tsaro, amma kuma yanzu al'umma sun zura ido, dan ganin matakan da mahukunta za su kara dauka na kare rayuwa da dukiyoyi wanda ake ganin nauyi ne da ya rataya wuyan gwamnati.